An kaddamar da matatar mai a Nijar

Taswirar Nijar
Image caption Taswirar Nijar

Yau aka kaddamar da matatar man petur ta farko a jamhuriyar Nijar.

Matatar man petur din da ke garin Danbaki a jihar Damagaram, wadda hadin gwiwa ce tsakanin Nijar da wani kampanin mai na kasar Sin, zata rika tace ganga dubu ashirin na mai a kowace rana.

Shugaban kasar ta Nijar, Issoufou Muhammadou ne ya jagoranci bikin kaddamarwar.

Sai dai ana cewa 'yan adawa sun kaurace ma bikin, haka nan kuma mutanen Damagaram ba su fito sun yi ma shugaban kasar maraba ba.

Gwamnatin ta ce zata mayar da farashin man ya koma 570 CFA kan kowace lita, daga 655 CFA, sakamakon korafin da jama'a ke yi cewa ya yi tsada.

Karin bayani