Likitoci sun ce Breivik na fama da tabin hankali

Hakkin mallakar hoto AFP

A kasar Norway, likitoci masu kula da mutanen da ke fama da tabin hankali sun ce, mutumin nan da ya kashe mutane saba'in da bakwai a watan Yuli, yana fama da tabin hankali a lokacin da ya yi aika-aikar.

Likitocin sun gano cewa, Anders Behring Breivik, yana fama da wani nau'in tabin hankali, wanda sakamakonsa ya sa shi tunanin cewa, an zabe shi a matsayin macecin jama'ar kasar Norway.

Likotoci sun ce cutar ta kuma Mista Breivik ganin cewa shine wanda zai yanke hukunci a kan wanda ya kamata ya mutu ko yayi rai.

Amma kuma duk da haka, a watan Afrilun badi ne zai gurfana a gaban kotu, inda za a tuhume shi da laifin dana bom a birnin Oslo, da kuma bindige mutane da yawa a tsibirin Utoeya.

Mai gabatar da kara na kasar Norway ta ce, idan daga karshe an yanke shawarar cewa, Breivik na fama da tabin hankali, to za'a nemi kotu da ta yanke hukuncin cewa, dole a tsare shi a asibitin masu fama da tabin hankali.

Karin bayani