Ana taro kan inganta muhalli a Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto EIA
Image caption Muhalli

A ranar Litinin ce dubban masana da wakilan gwamnatoci daga sassa daban-daban na duniya, za su fara wani taro a kasar Afirka ta kudu, a kokarin cimma wata yarjejeniya kan yadda za a shawo kan matsalar sauyin yanayi.

Mahalarta taron dai za su tattauna a kan batutuwa da dama cikinsu har da yadda za a rage yawan iska mai gurbata muhalli da kasashe masu arzikin masana'antu ke fitarwa.

Daya daga cikin masu halartar taron, Christine K., ta kugiyar kare muhalli da ke Jamus, ta shaida wa Nasidi Adamu Yahya cewa dole ne gwamnatoci su fitar da hanyoyin magance matsalolin da ke addabar muhalli, musamman a nahiyar Afirka.

Nahiyar dai ta fi fuskantar illolin da ke tattare da sauyin yanayi, wadanda suka hada da kwararowar hamada, da ambaliyar ruwa, da karancin ruwan sama, da kuma rashin sanin tabbas na samun kayan amfanin gona.

Karin bayani