An kammala zabe a Congo

Hakkin mallakar hoto
Image caption Joseph Kabila

An kawo karshen zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

An kyale mutanen da ke cikin layi a lokacin da wa'adin kammala zaben ya cika, su kada kuri'unsu.

Sai dai kuma jagoran 'yan adawa Etienne Tshisekedi ya ce 'yan sanda basu barshi ya kada kuri'ar sa ba a rumfar da yake so.

Ba'a samu rohotannin tashin hankali ba babban birnin kasar, Kinshasa.

Amma an bada labarin karawa a garin Lubumbashi dake kudancin kasar.

'Yan takara goma ne ke kalubalantar shugaba mai ci Joseph Kabila wanda ya shafe shekaru goma yana mulkin kasar.

An kawar da yiwuwar barkewar yaki

An yi ta rade-radin cewa za a dage zaben, saboda tsoron barkewear yaki, bayan da aka fuskancin tashe-tashen hankula gabanin zaben.

Hukumar zaben kasar ta fuskanci matsaloli da dama wajen aikewa da kayayyakin zabe, musamman a yankunan da ke da sarkakiya.

'Yan kasar sun fi kowa matsuwa wajen ganin an gudanar da zaben, suna masu cewa sauyi kawai suke bukata.

Sun ce gwamnatin kasar bata aiwatar da muhimman ayyuka ba duk kuwa da dimbin albarkatun kasar da Allah ya horewa mata.

Karin bayani