Jama'a sun fito sosai a zaben Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu kada kuri'a a Masar

A Masar, jama'a sun nuna zumudi a zaben farko na majalisar dokokin kasar, tun bayan da aka kawar da shugaba Hosni Mubarak a watan Fabrairu.

Dimbin jama'a ne suka fito domin kada kuri'unsu, kuma an ga dogayen layuka na jamaar da ke jefa kuri'a a tsanake, a rumfunan zabe.

Gidan talabijin din kasar ya bada sanarwar kara lokacin yin zaben, har zuwa karfe tara agogon Masar din, saboda yawan jama'a, da kuma jinkirin da aka samu tun farko.

Rahotanni sun ce, an sami karancin takardun zabe da kuma tawada.

A garin Assiut, sojoji sun ce komi ya koma daidai, bayan wani lamari na harbe-harbe da ya faru.

Karin bayani