Tubali tsakanin China da Amurka

Shugabannin kasashen BRICS Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daga hagu: Shugaba Dmitry Medvedev na Rasha, Shugaba Hu Jintao na China, Shugaba Dilma Roussef ta Brazil, da Firayim Minista Manmohan Singh na Indiya

Ba ko tantama harkokin tattalin arziki na gusawa zuwa kasashen da tattalin arzikinsu ke tasawa. A shekaru hamsin na farkon karni na ashirin da daya, tattalin arzikin kasashen Yamma ya dunkule wuri guda saboda kasashen ne ke kan gaba wajen ci gaba.

Amma a yanzu labari ya sha bamban.

Kamfanin Goldman Sachs, wanda ya harhada haruffan da suka ba da "BRIC" (kalmar brick a harshen Ingilishi na nufin 'jan tubali')—wato Brazil, da Rasha, da Indiya, da China a matsayin kasashe masu karfin fada-a-ji ta fuskar tattalin arziki—ya ce nan da shekara ta 2050 wadannan kasashe (yanzu an kara Afirka ta Kudu sun zama BRICS) za su sha gaban kasashen da suka ci gaba ta fuskar tattalin arziki, ciki har da Japan.

Tuni dai yawan kayayyakin da Indiya ke sarrafawa ya zarta na Jamus, yayin da gudmmawar China ga tattalin arzikin duniya ke karuwa har ta dara ta Amurka.

A wurin taron kasashen duniya ashirin masu karfin tattalin arziki (G20) na baya-bayan nan ma, kasashen Turai sun tunkari Indiya da China da bukatar taimako don warware matsalar kudin da addabe su. Babu wanda zai taba tunanin faruwar haka shekaru talatin da suka wuce.

Babu abin da ke jawo alaka ta kut-da-kut tsakanin mabambantan al'adu kamar kasuwanci. Don haka ba abin mamaki ba ne idan kasashe kamar China, da Indiya, da Rasha, da Brazil suka haed wuri guda.

Biyu daga cikin kasashen na BRICS dai, wato Indiya da China, manyan kasashe ne masu shigo da makamshi yayin da bitu daga cikinsu kuma, wato Rasha da Brazil, manyan masu fitar da makamashi ne.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wani ma'aikacin banki na karbar kudin Rupee na Indiya a Mumbai

Rasha na da dimbin albarkatun man fetur da gas, yayin da Brazil ke da ma'adanai da dama ciki har da tama da karafa.

Saboda haka wadannan kasashe ba su da wani zabi illa su hada karfi da karfe da ciyar da juna gaba.

Indiya da China ma na da alaka ta cude-ni-in-cude ka: Indiya a bangaren hidima, China kuma a bangaren kere-kere.

A shekrau goma sha-biyar din da suka gabata, cinikayya tsakanin Indiya da Japan kusan ta cije, amma cinikayyarta da China kusan ta yi ta rubanya duk shekaru, har ma ana sa rai za ta kai dala biliyan 100 a shekara ta 2013.

A shekaru biyar masu zuwa Indiya na bukatar samar da mega watt 1,000,000 na wutar lantarki, kuma kashi ashirin cikin dari da dukkan na'urorin da ta ke bukata don cimma hakan na zuwa ne daga China.

Sai dai kuma, ta yaya wadannan kasashe na BRICS za su kaucewa tayar da jijiyoyin wuya ta fuskar siyasa a tsakaninsu?

Babu shakka akwai tayar da jijiyoyin wuya tun da wannan kungiya ba aba ce wadda gwamnatoci suka tsara ba, igiyar ruwan kasuwa ce kawai da kuma hadewar duniya wuri guda suka samar da ita.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata masana'anta a Indiya

Ana kallon Indiya da China a matsayin kasashe biyu da ke matukar gasa da juna ta fuskar tattalin arziki a yankin, amma kuma a lokaci guda dole na sa su hada kai a kan batutuwa da dama.

Sun dai yi aiki tare a fagage da dama na duniya kamar Kungiyar Cinikayya ta Duniya, wato WTO, da kuma a kan batutuwa da dama kamar sauyin yanayi.

Indiya da China na kuma fuskantar kalubale iri guda ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki, don haka su kan hade kai in sun zo tattaunawa da kasashen da suka ci gaba.

Wannan ne ya sa sau da dama a kan kwatanta dangantakarsu da cewa hada-gasa--wasu hadin kai da kuma gasa a lokaci guda.

Kasashe da dama na hada karfi ta fuskar tattalin arziki da Indiya da China, amma kuma su kan dogara a kan Amurka ta fuskar tsaro. Wannan ya kawo wani sabon zubi a fagen siyasar duniya.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kasashen BRIC

Yayin da kasashen na BRICS ke kara dankon cinikayya a tsakaninsu, suna kuma kulla alaka ta da kasashen Gabas mai nisa masu tashe ta fuskar tattalin arziki, irinsu Korea ta Kudu, da Indonesia, Vietnam, da Japan.

Sai dai kuma wadannan kananan kasashen na juyawa ne wurin Amurka don ta jagoranci sabon tsarin tsaro a yankin Pacific.

Indiya ma, ko da yake cinikayya tsakaninta da China ta zarta wadda ke tsakaninta da Amurka shekaru biyu da suka gabata, ta kan karkata ne ga Amurka idan ana batun hadin-kai ta fuskar nukiliya da tsaro a yankin Tekun Indiya da Pacific.

Ko ba komai dai a wannan yankin ne hanyoyi mafiya muhimmanci na safarar makamashi da kayayyaki dama su ke.

Kasashen BRICS ne dai ke da kashi arba'in cikin dari na al'ummar duniya da kuma kashi ashirin da biyar na kayayyakin da ake sarrafawa a duniya.

Sannan kuma, yayinda al'ummun Turai da Amurka za su tsufa a shekaru masu zuwa, yawan masu sayen kaya a wadannan kasashe karuwa ya ke yi koyaushe.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firayim Ministan Indiya, Manmohan Singh

Babu shakka nan ba da jimawa ba, Indiya da China za su fara kankane kasuwannin hadahadar kudade na duniya. Don haka kayyade farashin kayayyaki, da na fetur, da ma'adanai da a yanzu haka ake yi a cibiyoyin hadahada na Amurka da ke Wall Street zai koma nahiyar Asiya.

To amma kafin hakan ya tabbata, sai Indiya da China sun kara bude kasuwanninsu; suna kuma bukatar samar da hanyoyin saukaka hadahadar kadarori a bisa farashin da kasuwa ta kayyade.

Za su kuma bukaci samar da cibiyoyin hadahadar kudade masu karfi wadanda za su saukaka wannan juyin waina a tattalin arzikin duniya.