'Ana tsare da fursunoni 7,000 a Libya'

'Ana tsare da fursunoni 7,000 a Libya' Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ne rahoto na farko da Majalisar ta fitar kan Libya tun bayan yakin kasar

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce mayakan gwamnatin NTC ta Libya na ci gaba da tsare kimanin fursunoni 7,000 ba bisa ka'ida ba.

Wannan shi ne karo na farko da majalisar Dinkin Duniya ke fitar da rahoto tun bayan kare yakin da aka yi a kasar ta Libya, wanda aka kwashe watanni takwas ana yi.

A makon jiya dai, jakadan Majalisar Dinkin Duniya da ke Libya ya yi marhabin da gwamnatin rikon kwaryar da aka girka a Libyar, sai dai ya ce kalubalen da kasar ke fuskanta na da yawa.

Rahoton dai ya kiyasta cewa fursunoni dubu bakwai ke tsare a gidajen yari, da kuma wasu wuraren tsare jama'a na wucin gadi da ke fadin kasar, wadanda ke karkarshin mayakan gwamantin kasar.

An ci zarafin fursunonin

Ana zargin mayakan da muzgunawa wasu daga cikin fursunoni, wadanda akasarinsu 'yan kasashen Afirka ne da ake zargi da kasancewa sojojin haya.

Yawancin fursunonin dai, in ji rahoton, basa samun adalci, domin kuwa rundunar 'yan sanda da kuma kotunan kasar basa aiki.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya da ke Libya, Ian Martin, ya ce sababbin ministocin da gwamnatin kasar ta nada, sun ce za su dauki mataki, a lokacin da ya gabatar musu da wannan korafi:

"Hakan wata alama ce da ke nuna cewa an samu bambanci ga yadda gwamnatin baya ta tafiyar da lamura, tun da dai hukumomi basu musanta cewa ana cin zarafin bil adama ba".

Sabon ministan cikin gida na kasar ya shaida wa jakadan Majalisar cewa, yana maraba da irin sukar da aka yi musu, kuma hakan zai kara musu kwarin gwiwa na magance matsalar.

Sai dai Mr Martin ya shaida wa kwamatin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa, duk da irin kimar da gwamnatin Libya ke da ita, tana fuskantar babban kalubale game da yadda za ta kwance damarar mayakanta, kana ta basu ayyukan yi, ganin cewa suna daukar doka a hannunsu.

Karin bayani