Kenya ta yi watsi da sammacin kama Albashir

Image caption Shugaban Sudan, Omar el-Bashir

Kenya ta ce ba za ta yi aiki da hukuncin da wata kotu a kasar ta yanke ba, wanda ke ba da umarnin tsare shugaban Sudan, Omar Hassan Elbashir.

Hakan ya sa Sudan din umartar jakadan Kenya a Khartum da ya bar kasar.

Ministan harkokin wajen Kenya Moses Wetangula ya shaidawa BBC cewa kasar sa zata yi aiki ne da matsayin kungiyar tarayyar Afrika da ya yi watsi da sammacin kama shugaban Sudan din da kutun hukunta masu laifukan yaki ta fitar.

Kotun duniya na neman el-Bashir

Da ma dai kotun hukunta masu aikata laifukan yaki ta duniya na neman shugaba Bashir, inda ta ke zarginsa da aikata laifukan da suka hada da kisan kare dangi, da laifukan yaki, da kuma laifukan cin zarafin bil adama, wadanda ta ce ya aikata a Darfur.

Shugaba Bashir dai ya yi balaguro zuwa Kenya a watan Agustan bara, kuma ba a kama shi ba.

Kuma bayan wancan balaguron ne, reshen kungiyar masu taimakawa alkali da ke Kenya, ya nemi kotun da ta bayar da sammacin kama shi.

Da fari dai ma'aikatar harkokin waje ta Kenya bata son aiwatar da umarnin, tana mai cewa batun ya shafi cikin gidanta ne kawai, don haka ba zai shafi dangantakarta da wata kasa ba.

Kimar shugaba Bashir dai ta ragu a idanun duniya, tun bayan kotun hukunta masu aikata laifukan yaki ta duniya, ta bayar da sammmacin kama shi.

Sai dai ya na samun goyon baya daga kasashen Larabawa da dama, da kasashen Afirka, da kuma China.

Karin bayani