Za a yi taro game da tattalin arzikin Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabannin kasashen Turai

A ranar Talata ce ake sa ran ministocin kudi na kasashen da ke amfani da kudin euro, za su amince da hanyoyin da za a bunkasa asusun ceto tattalin arziki na kungiyar.

Idan ministocin suka amince da shirin a Brussels, asusun na European Financial Stability Fund, zai samu karin kudi daga hukumomin gwamnati - sannan ya bayar da kariya ga masu zuba jarin da suke sayen takardun lamuni na gwamnatoci.

Sai dai halin da kasuwannin kudin kasashen Turai ke ciki, ya sa zai yi wuya a cimma burin da ake da shi na bunkasa kudin asusun zuwa euro tiriliyan guda.

Kasashen Turai da dama dai, musamman wadanda ke amfani da kudin bai-daya na euro, na fama da kangin tattalin arziki.

Karin bayani