An samu karuwar ruwan sama a Gabashin Afirka

Fari Hakkin mallakar hoto BBCPersian.com
Image caption An samu karuwar saukar ruwan sama a Gabashin Afirka

Cibiyar bada agaji ta gwamnatin Amurka USAID ta ce an samu karuwar saukar ruwan sama a yankin gabashin Afirka dake fama da fari idan aka kwatanta da bara.

A kiyasinta, Cibiyar USAID ta ce tun daga watan Oktoba yawancin yankunan, ciki har da Kenya da Somalia da kuma Habasha sun samu nunkin saukar ruwan sama, abinda kuma zai taimakawa yabanya.

Amma duk da haka USAID din tayi gargadin cewa idan aka cigaba da ruwan sama kamar da bakin kwarya, akwai yiwuwar a samu ambaliyar ruwa daga tafkin Victoria, abinda kuma zai iya kawo tsaiko wajen ayyukan jin kai.

Karin bayani