Taron ministocin kudi na Tarayyar Turai

Ministan kudin Jamus, Wolfgang, Schaeuble Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ministan kudin Jamus, Wolfgang, Schaeuble

Ministocin kudi na kungiyar tarayyar Turai na yin wani taro a Brussels,yayinda wani babban jami'i ya yi gargadin cewar, kungiyar na da yan kwanaki ne kawai na daukar kwakkwaran matakin warware matsalar bashi.

Kwamishinan harkokin kudi na Kungiyar, Olli Rehn, ya ce kasashen dake amfani da kudin Euro, na shirin shiga cikin wasu kwanaki goma masu mahimmancin gaske.

A jiya kasashen masu amfani da kudin Euro, sun amince da wasu matakai na bunkasa asusun cetonsu, ko da yake sun amince cewa, ba zai kai adadin Tiriliyan din da suke hankoron samu.

A maimakon hakan suna fatan samun karin taimako daga asusun bayar da lamuni na IMF.

Karin bayani