Tuhuma a kan Laurent Gbagbo

Laurent Gbagbo Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Laurent Gbagbo

Kotun duniya mai hukunta miyagun laifufuka, ICC ta ce tsohon shugaban Cote D'Ivoire Laurent Gbagbo yana fuskantar tuhuma bisa aikata laifufuka hudu na cin zarafin BiAdama da suka hada da kisa da kuma fiade.

Yanzu haka dai Mr Gbagbo din yana tsare a birnin Hague, bayan da aka kama shi a jiya a kasar ta Cote D'Ivoire.

Babban mai shigar da kara na kotun, Luis Moreno- Ocampo ya ce akwai hujjar dake nuna cewa da gangan magoya bayan Mr Gbagbo din suka kitsa tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa a bara.

Mutane kusan dubu uku ne suka rasa rayikansu a sanadiyyar tashin hankalin da aka shafe watanni ana yi.

Mr Moreno -Ocampo ya ce duka bangarorin biyu sun aikata laifufuka saboda haka akwai yiwuwar kotun ta ICC ta fitar da wasu karin takardun sammancin kama wadanda ake zargi.

Karin bayani