Laurent Gbagbo ya isa Netherlands

Tsohon Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo
Image caption Laurent Gbagbo zai gurfana gaban kotun manyan laifuka dake Hague

Wani jirgin sama da ke dauke da tsohon Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo ya sauka a Netherlands.

Hakan dai ya biyo bayan rahotannin dake cewar za a mika Mista Gabgbo ga jami'an kotun hukunta mugayen laifuka wato ICC dake Hague.

Babban mai shigar da kara a kotun, Lius Moreno Ocampo ya dade yana binciken zargin cewar magoya bayan Gbagbo na da hannu wajen kashe-kashe da fyaden da aka yi bayan zaben Shugaban Kasar a bara.

An dai kashe fiye da mutane dubu uku a tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaben shekarar 2010, bayan da Laurent Gabago yaki amincewa da cewar ya sha kayi a zaben Shugaban Kasar

Yanzu haka dai ana fargabar mai yiwuwa wannan tuhuma da kotun manyan laifukan za ta yi masa, ka iya sake rura wutar wani sabon rikicin a Kasar ta Ivory Coast

Karin bayani