Hamid Karzai ya mika kokon bara a Bonn

Hamid Karzai Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan

Shugaba Hamid Karzai na afghanistan ya ce goyon bayan kasashen duniya bayan janyewar dakarun NATO daga kasarsa a shekarar 2014 na da matukar muhimmanci ga zaman lafiyar kasar.

Da wadannan kalamai ne dai ya bude taron duniya a kan makomar Afghanistan a birnin Bonn na kasar Jamus.

Taron na zuwa ne bayan shekaru goma da gudanar da makamancinsa, 'yan makwanni bayan kifar da gwamnatin Taliban.

Sai dai Pakistan, wadda ke da muhimmiyar rawar da za ta taka a makomar Afghanistan din, ba ta halarci taron ba don nuna rashin amincewarta da harin da kungiyar NATO ta kai a kan wani shingen binciken motoci a watan jiya.

Kungiyar ta NATO dai ta nemi afuwa dangane da harin na 26 ga watan Nuwamba wanda a lokacinsa sojojin Pakistan ashirn da hudu suka rasa rayukansu, ranar Lahadi kuma Shugaba Barack Obama na Amurka ya yi jaje ga iyalan wadanda abin ya shafa, amma Pakistan ta nace cewa ba za ta sauya ra'ayinta ba dangane da tattauanawar.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Daga hagu: Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan, da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, da kuma Ministan Harkokin Wajen Jamus, Guido Westerwelle

Shugaba Karzai ya yaba da ci gaban da Afghanistan ta yi a shekarun goman da suka biyo bayan taro na farko, sai dai kuma ya yi gargadin cewa duk da haka da sauran aiki a gaba. Don haka, a cewarsa, wannan taro zai baiwa Afghanistan dama ta karfafa ci gaban da aka samu.

"Mutanen Afghanistan sun zuba ido su ga tabbacin da wannan taro zai bayar dangane da tsaron kasa da ci gaban tattalin arziki", in ji Mista Karzai.

Ya kuma kara da cewa kasarsa ba ta so ta zamewa kasashen duniya wani nauyi na daidai da kwana guda fiye da yadda ya wajaba, amma kuma a cewarsa kasar za ta bukaci taimako na akalla shekaru goma nan gaba.

Yayinda akae gudanar da taron dai Amurka da ma wadansu kasashe sun lashi takobin ci gaba da tallafawa farfadowar Afghanistan bayan shekara ta 2014.

A cewar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, "Amurka ta dauki aniyar ci gaba da dafawa abokananmu da ke Afghanistan".

Misis Clinton daya ce daga cikin mahalarta taron su dubu daya daga kasashe da kungiyoin kasa-da-kasa guda dari.

Shugaban na Afghanistan ya kuma yi shagube da abin da ya kira "matsalar maboyar 'yan ta'adda a wajen Afghanistan", wadda ya ce har yanzu ba a magance ta ba kuma tana barazana ga tsaron yankin, da ma duniya baki daya.

Masu sharhi dai sun ce in dai ana so a tattauna da Taliban don samar da zaman lafiya-abin da Mista Karzai ya ce babu gudu, ba ja-da-baya-to Pakistan na da matukar muhimmanci.

Jami'an Afghanistan da na Amurka sun sha bayyana cewa sojojin sa-kan da ke yaki a Afghanistan daga Pakistan suke shiga-zargin da Pakistan ta musanta.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wakilan Afghanistan a wurin baban taron na Bonn

Mai yiwuwa a samu muhimman batutuwa da dama a ajandar taron, amma mafi muhimmanci a cikinsu su ne batun sasantawa da Taliban da kuma batun kudin da za a kashe don sake ginin Afghanistan din bayan shekarar 2014.

An kiyasta cewa za a bukaci fam miliyan dubu hudu da dari biyar duk shekara in dai ana so kasar ta ci gaba da bunkasa yadda ta ke yi yanzu.

Ya zuwa yanzu an kashe sojojin NATO fiye da dari biyar a bana a Afghanistan. Akasarin fada mafi muni a yakin da aka kwashe shekaru goma ana yi an fafata shi ne a gabashin kasar, kusa da kan iyaka da Pakistan.

"Manufar mu ita ce samar da zaman lafiya a Afghanistan ta yadda ba za ta sake zama mafaka ga 'yan ta'adda ba", in ji Ministan Harkokin Wajen Jamus, Guido Westerwelle.

Tuni dai an yi nisa da yunkurin kaddamar da tattaunawa da Taliban, sai dai har yanzu babu wani sakamako a kasa

Yunkurin sasantawa ya ci karo da babban koma-baya a watan Satumba, lokacin da aka yiwa tsohon shugaban kasar, Burhanuddin Rabbani, kisan gilla yayin da ya ke jagorantar shirin sasantawa da masu tayar da kayar baya.

"Yanzu haka ba mu san adireshinsu ba. Babu inda za mu je mu kwankwasa", in ji jakadan Afghanistan a Amurka, Eklil Hakimi, a wata hira da kamfanin dillancin labarai na AP.

Amurka da ma sauran kasashen Yamma sun jima suna zargin Pakistan da baiwa Taliban da sauran kungiyoyi masu tayar da kayar baya, ciki har da Kungiyar Hakkani wadda ake zargi da kai hare-hare a Afghanistan, mafaka.

Duk da haka masu sharhi sun ce yana da muhimmanci a samu hadin kan Pakistan in har ana so a samu ci gaba a kokarin zaman lafiya da Taliban.

Masu aiko da rahotanni sun ce rashin shigar da Taliban shirin zaman lafiyar zai sa a sha wahala wajen samun hadin kai a yunkurin sake gina Afghanistan.

Karin bayani