An yankewa Ali Konduga hukunci a Abuja

Alhaji Sanda Konduga
Image caption Mahaifin Ali Sanda Konduga (Al-Zawahiri), Alhaji Sanda Konduga

Wata kotu a Najeriya ta yankewa Ali Sanda Konduga, wanda ke ikirarin magana da yawun kungiyar nan ta Jama'atu Ahlissunah Lidda'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram, hukuncin daurin shekaru uku a gidan kaso.

Shi dai Ali Sanda Konduga, wanda aka fi sani da Alzawahiri, ya amsa aikata laifukan da ake tuhumar sa da aikatawa a ranar ashirin da biyu ga watan da ya gabata; laifukan da suka danganci aikewa da sakwannin barazana ga wasu 'yan siyasa ta hanyar sakon wayar salula na text a lokacin da hukumomin suka ce ya yi ikirarin yana magana da yawun kungiyar Boko Haram.

Sai dai a baya kungiyar ta Boko Haram ta nesanta kanta da shi Al-zawahirin, tana cewa ba ya magana da yawunta, kuma ma ta yi zargin cewa jami'an tsaro ne suka dasa shi domin ya rika ikirarin magana a madadinsu.

A zaman kotun na yau Talata, Konduga ya roki kotun ta yi masa sassauci, sannan ya yi alkawarin baiwa jami'an tsaro hadin kai wajen magance matsalar Boko Haram.

Hakan ne ya sa mai shari'a Oyebola Oyewumi ta ce ta yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a gidan kaso, sabanin shekaru taran da za a iya yanke masa.

Ya zuwa yanzu dai ba tabbacin ko akwai wata yarjejeniya a tsakanin Konduga da hukumar leken asiri ta SSS.

A karshen mako ne dai mahaifin Al-Zawahiri, Alhaji Sanda Konduga, ya ce dan nasa yana fama da tabin hankali, kuma za su yi nazarin duk wani hukunci da aka yanke masa.

A zaman kotun na watan da ya gabata, Sanata Ali Ndume, wanda ake tuhuma tare da Konduga, ya musanta aikata laifin mika bayanan sirri ga mutumin da bai kamata ba da kuma barazana ga wadansu 'yan siyasa.

Hukumomi dai sun janye karar da suka shigar da sanatan a gaban kotun Majistire sannan suka shigar da wata sabuwar kara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a wannan makon.

Sai dai har yanzu sanatan bai gurfana a gabanta ba don amsa laifi ko akasin hakan.

Sababbin laifuffukan da ake zargin Sanata Ali Ndume da aikatawa, wadanda aka shigar a gaban Babbar Kotun ta Tarayya, sun hada da bayar da lambobi ga Ali Konduga da kuma rashin bayar da bayanai a kan 'yan ta'adda ga jami'an tsaro, abin da ya saba da tanade-tanaden dokar yaki da ta'addanci.

Karin bayani