Manyan jam'iyyun siyasar Rasha

Sakamakon zabe Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sakamako na farko da aka kafe a kofar ofishin Hukumar Zabe ta Rasha

An yi zaben majalisar dokoki a Rasha wanda zai fasalta yadda Majalisar Wakilan kasar, Duma, za ta kasance a shekaru biyar masu zuwa. Ko wadanne ne manya a cikin jam'iyyun da za su taka rawa a majalisar?

Ana daukar jam'iyyar United Russia a matsayin jam'iyyar da ke marawa Vladimir Putin baya. Manufarta ta siyasa ita ce mara baya dari bisa dari ga gwamnati da kuma harkokin da ke da alaka da hakan.

Daya daga cikin fitattun abubuwan da suka bambanta ta da sauran jam'iyyu shi ne goyon bayan Firayim Minista Vladimir Putin. Sai dai kuma watanni uku kafin zaben shugaban kasa sunan Shugaba Dmitry Medvedev ne farko a jerin 'ya'yanta.

A 'yan kwanakin nan dai jam'iyyar United Russia ta yi yunkurin tallata kanta a matsayin jam'iyya mai ra'ayin 'yan mazan-jiya.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Firayim Minista Vladimir Putin lokacin da ya kai ziyara ofishin United Russia ranar Asabar

Sai dai kuma jam'iyya ce da ke ikirarin kare hakkokin talakawa, don haka a lokacin zabe ta kan yi amfani da ruhin ksihin kasa ta shiga fagen masu ra'ayin gurguzu.

A nan ne take alkawarin ci gaba da samarwa talakawa ababen more rayuwa da kuma kurarin cewa "Rasha za ta farfado daga suman da ta yi".

A shekarar 2001 aka kafa jam'iyyar United Russia—lokacin da aka hade jam'iyyun Unity da Fatherland.

Mutane da dama dai na ganin jam'iyyun sun hade ne saboda matsin lambar fadar gwamnati ta Kremlin.

A shekarar 1999 shugaban kasar a lokacin, Boris Yeltsin, da mukarrabansa suka kirkiri jam'iyyar Unity, wacce ita ce kashin bayan dinkewar; an kuma kirkireta ne don ta yi gogayya da hadin gwiwar jam'iyyun Fatherland da All Russia, wadanda ke kara karfi a karkashin jagorancin Magajin Garin Moscow Yuri Luzhkov da tsohon Firayim Minista Yevgeny Primakov.

Image caption Magoya bayan Jam'iyyar Kwaminis ta Rasha suna wani gangami

Jam'iyyar Kwaminisanci ta Tarayyar Rasha, wadda aka kafa a shekarar 1993, ita ce a hukumance ta gaje matsayin Jam'iyyar Kwaminis ta Tarayyar Soviet.

Dangane da batun tattalin arziki dai jam'iyyar ra'ayin gurguzu ne da ita. A kundin tsarin mulkinta, ta yi kira a samar da wani "sabon tsarin gurguzu" a Rasha; a cewarta, tsarin jari-hujja na shure-shuren mutuwa kuma ya kamata gwamnati ta karbe iko da dukkan masana'antu.

Kishin kasar Rasha ne dai kashin bayan akidar jam'iyyar; ta wannan kuma ta kaucewa manufar Makisanci wanda hantsi ne, leka gidan kowa.

A bisa al'ada, jam'iyyar na jan hankalin mutanen da ke kawazucin zamanin Tarayyar Soviet.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A shekarar 1996, shugaban jam'iyyar na tsawon lokaci, Gennady Zyuganov, na cikin 'yan takarar shugaban kasa na gaba-gaba. Amma tun bayan hawan Vladimir Putin karagar mulki, tasirin Jam'iyyar Kwaminisancin ya ragu matuka.

Duk da haka, idan aka yi la'akari da yawan wakilai a cibiyoyi na hukuma, har yanzu Jam'iyyar Kwaminisancin ce ta biyu a karfi a tsakanin jam'iyyun Rasha.

A zaben majalisar dokokin da aka yi ranar Lahadi dai, yawan kuri'un da jam'iyyar ta samu sun kusan rubanya wanda ta samu a zaben 2007.

A cewar masu sharhi a kan al'amuran siyasa da dama, da Jam'iyyar Kwaminisancin ta rikide ta zama irin jam'iyyun gurguzu na Turai a maimakon ta rika fakewa da Josef Stalin, da ta samu kyakkyawar damar sake komawa kan mulki.

Jam'iyyar A Just Russia ta samo tushe ne daga hadewar wasu kananan jam'iyyu uku masu matsakaicin ra'ayi a shekarar 2006.

Da farko dai an zaci fadar gwamnati ta Kremlin ce ta assasata da nufin zaizaye kuri'un Jam'iyyar Kwaminisanci da kuma nuna cewa ana gudanar da tsarin siyasa mai jam'iyyu biyu.

A watan Maris na shekarar 2006, babban mashawarcin shugaban kasar Rasha ta fuskar siyasa, Vladislav Surkov, ya ce akwai bukatar "kafa [ta siyasa] ta biyu wadda kasar za ta iya tsayawa a kanta idan ta farko (United Russia) ta yi tsami".

Ga alamu, daga baya mahangar Kremlin din ta sauya.

Idan da Vladimir Putin ya ce yana kaunar United Russia da A Just Russia daidai-wa-daidai a jajibirin zaben majalisar dokoki a shekarar 2001, da ya taimaka wajean assasa tsarin jam'iyyu biyu.

Amma sai Mista Putin ya alakanta kansa da United Russia kawai.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban A Just Russia, Sergei Mironov

Shugaban A Just Russia, Sergei Mironov, ya yi kakkausan suka a kan jam'iyyar United Russia da ma wasu shawarwari da gwamnati; ya ambaci gazawa a ayyukan gwamnati mai ci, amma bai taba yin magana a kan Vladimir Putin da Dmitry Medvedev.

Mista Mironov abokin Putin ne tun tsakiyar shekarun 1990.

A farkon shekarar 2011 Miranov da Putin suka babe, al'amarin da ya sa wasu ke tunanin jam'iyyarsa za ta sha mummunan kaye a zaben majalisar dokoki na ranar 4 ga watan Disamba.

Sai dai jam'iyyar ta baiwa mara da kunya da yawan kuri'unta ya rubanya wanda ta samu a 2007; da haka kuma ta zama jam'iyya ta uku mafi girma a kasar.

Manazarta da dama dai na alakanta wannan nasara da kuri'un da wadanda ke ganin babu wani dan takara na daban, musamman masu sassaucin ra'ayi, suka kada don nuna rashin amincewa da United Russia.

In aka manta da cewa Jam'iyyar Kwaminisanci ta samo asali ne daga kungiyar siyasa ta Lenin, to Jam'iyyar Liberal Democrat ce ta fi ko wacce dadewa a Rasha.

A shekarar 1990 Vladimir Zhirinovsky, wanda a lokacin ba a san shi sosai ba, ya yiwa jam'iyyar rajista, kwana kadan bayan kaddamar da tsarin jam'iyyu masu yawa a kasar.

Abokansa da dama sun ce da tabarrakin shugaban hukumar leken asiri ta KGB a wancan lokacin, Vladimir Kryuchkov, aka kirkiri jam'iyyar, ko da yake babu wata hujjar da ke tabbatar da hakan.

Akidar jam'iyyar dai ta 'yan mazan jiya ce; babu abin da ya hada ta da sassaucin ra'ayi ko ma dimokuradiyya.

Masu adawa da ita sun yiwa jam'iyyar ba'a da cewa tana alkawarta samarwa ko wacce mace miji, ko wanne namiji kuma kwalbar giya ta vodka.

A zabukan majalisar dokoki na jihohi a watan Disamban 1993 jam'iyyar ta samu kashi ashirin da uku cikin dari na kuri'un da aka kada; har yanzu kuma ba ta sake yin irin wannan nasara ba.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jagoran Jam'iyyar Liberal Democrat, Vladimir Zhirinovsky

Zhirinovsky ne kadai dan siyasar Rasha da ya tsaya takara a dukkanin zabukan shugaban kasar da aka gudanar (banda na 2008).

Ya yi kaurin suna wajen aikata abin kunya, da fadace-fadace, da halaye masu ban takaici. Ya kan yi kakkausar suka a kan 'yan Jam'iyyar Kwaminis da ma masu sassaucin ra'ayin da ke goyon bayan kasashen Yamma, amma idan zai yi magana a kan gwamnati mai ci ya kan tausasa lafazinsa. Bayan haka kuma 'ya'yan jam'iyyar a Majalisar Wakilai ta Duma su kan biyewa muradun Kremlin.

A zabukan 4 ga watan Disamba yawan kujerun jam'iyyar Liberal Democrat ya karu daga kashi takwas cikin dari zuwa kashi goma sha daya cikin dari. A cewar kwararru, jam'iyyar ba ta da farin jini amma a kodayaushe tana samun goyon bayan wadanda ba manufofinta ne suka dame su ba, illa kawai suna sha'awar rashin kamun kan shugabanta.

Masu sharhi a kan al'amuran siyasa sun ce jam'iyyar na amfanar gwamnati saboda tana zaizaye kuri'u daga sauran jam'iyyun 'yan kishin kasa.

Karin bayani