Hillary Clinton na ziyara a Burma

Hillary Clinton a Burma Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hillary Clinton na wata ziyara mai cike da tarihi a Burma

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton na tattaunawa da Shugabannin Kasar Burma wadanda gwamnatinsu ke samun goyon bayan sojoji, a cigaba da ziyarar ta mai dimbin tarihi a Kasar.

A lokacin bude tattaunawar ta da Shugaban Kasar Thein Sein , Mrs Clinton ta bayyana masa cewar tana da kwarin gwiwa akan abinda gwamnatin Kasar ke yiwa mutanen Burma, inda ta bayyana ziyarar a matsayin wani sabon babin hulda tsakanin Kasashen biyu.

Ziyarar Hillary Clinton a Burma tukwici ne dangane da irin sauye-sauyen da suka wakana a Kasar

Daga bisani dai Mrs Clinton zata garzaya birni mafi girma a Kasar wato Rangoon, domin tattaunawa da jagorar 'yan adawa Aung San Suu Kyi.

Karin bayani