Za a tsaurara takunkumi a kan Iran

Wasu ministocin Tarayyar Turai Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu ministocin Tarayyar Turai

Jami'an Diplomasiya a Brussels sun ce ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince su tsaurara takunkumi a kan Iran saboda damuwa game da shirinta na nukiliya.

Sun kara saka karin sunayen kusan dari da tamanin na Kamfanoni da mutane a cikin jerin wadanda takunkumin zai shafa.

Ministocin sun kuma amince su ci gaba da aiki a kan sauran matakan da jami'ai suka ce za su iya shafar bangaren makamashi na Iran.

Taron na Brussels ya zo ne kwana 2 bayan masu zanga zanga a Iran sun afkawa Ofishin jakadancin Birtaniya a kasar, abin da ya sa Birtaniyar ta bada umurnin korar Jami'an Diplomasiyar Iran dake nan London.

Karin bayani