Taron samar da zaman lafiya a Arewa

Wani tankin yaki a Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wani tankin yaki a Najeriya

Masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a Najeriya, na gudanar da wani taro don musayar ra'ayoyi a kan hanyoyin da suka dace a bi don kawo karshen rikice-rikice a arewacin kasar.

A wajen wani taro na kwana guda da kamfanin jaridar People's Daily ya shirya a Abuja yau, ra'ayin mahalarta ya fi karkata ne ga magance talauci da rashin aikin yi da kuma samar da ilimi a yankin arewacin Najeriya a matsayin hanyar tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

A 'yan shekarun nan dai yankin na arewacin Najeriya ya sha fama da rikice-rikicen da ake alakanta su da addini ko kuma kabilanci ko ma siyasa.

Dubban mutane ne dai suka rasa rayikansu a sakamakon irin wadannan rikice-rikice a a yankin, tare da tafka asarar dukiya mai dimbin yawa.

Karin bayani