Za a dade kafin a gyara lamura a kasashe masu amfani da kudin EURO - Inji Merkel

Angela Merkel, Shugabar Gwamnatin Jamus Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Angela Merkel, Shugabar Gwamnatin Jamus

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta zayyana shawarwari a kan tunkarar matsalolin kudin da yankin Turai da ke amfani da kudin Euro ke fama da shi.

Babban abin da shawarar tata ta fi maida hankali a kai shi ne sauya yarjejeniyar Tarayyar ta Turai, domin a tilasta sanin ya kamata sosaia kan kasafin kudin gwamnatoci.

Masana tattalin arziki dayawa sun yi gargadin cewa, amfani da kudin bai daya, ba tare da an hade kasafin kudaden gwamnatoci ba, yana da hadari.

Kasashen yankin Euro sun yi kokarin shawo kan matsalar, ta hanyar bullo da dokokin da suka takaita yawan kudaden da kasa za ta iya rantowa.

To amma kasashen sun sha keta irin wadannan dokokin - cikinsu kuwa har da Jamus.

Don haka, a yanzu, shugabannin Jamus din da na Faransa na ta kara matsa kaimin a bullo da wani shiri mafi tasiri.

Akwai manyan bambance-bambance, dangane da yadda za a tabbatar da dokokin.

To amma yawancin kasashen dake amfani da kudin na Euro sun amince da gyaran da ake son yi.

Karkashinsa gyaran za a takaita yawan kudaden da za a iya ba gwamnati bashi, wadanda ba su wuce kima ba.

Karin bayani