Faransa da Jamus suna son sabuwar yarjejeniya don kare kudin Euro

Angela Merkel da Nicolas Sarkozy Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Angela Merkel da Nicolas Sarkozy

Shugabannin kasashen Faransa da Jamus sun ce suna son samar da wata sabuwar yarjejeniya mai karfin gaske, wadda zat a maido da amincewar da ake da ita a kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Bayan taron da suka yi a Paris, Nikolas Sarkozy da Angela Merkel, sun ce suna son a amince da yarjejeniyar nan da watan Maris na shekara mai zuwa.

Sun son a kara sa ido sosai a kan manufofin kudi da kuma kashe su a cikin kasashe goma sha bakwai da ke amfani da kudin na Euro.

Sun amince da a samar da hanyar ladabtarwa idan har gibin kasafin kudin wata kasa ya zarta adadin da aka kayyade na kashi uku cikin dari.

Kuma tilas ne tsarin mulkin kowace kasa ya hada da samar da daidaito a kasafin kudin kasar. Sai dai kuma editan BBC a nahiyar Turai ya ce babu daya daga cikin matakan da ya fayyace yadda za a rage dinbim bashin da ke kans