Za a kammala kwaso Alhazan Najeriya ranar 7 ga wata

Aikin Hajji Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hukumar Alhazan Najeriya zata kammala aikin kwaso Alhazan Kasar ranar 7 ga wata

Hukumar Alhazan Najeriya tace, ranar bakwai ga watan Disamba zata kammala aikin kwaso Alhazan Najeriya dake Kasa mai tsarki.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu rahotanni ke cewa, wasu Alhazan suna nuna rashin gamsuwa da jinkirin dawo da su gida, lamarin da aka ce ya jefa wasunsu cikin wani mawuyacin hali.

Keptin Shehu Iyal shine mai baiwa Shugaban Najeriya shawara akan harkar sufurin jiragen sama kuma mamba a hukumar aikin Hajjin Najeriya, ya kuma shaidawa BBC cewa su na da isassun jiragen da zasu kwaso Alhazan gida

Yace yanzu haka an dawo da Alhazan Najeriya gida su 70,286 cikin Alhazai 89,000 da suka sami tafiya ta hanyar hukumar su.

Dangane da rahotannin dake cewa wasu Alhazan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga kuwa domin nuna rashin jin dadin su, Keptim Iyal ya ce ba shi da masaniya dangane da wannan labari

Karin bayani