Ministocin kudi na Najeriya da Afirka ta Kudu sun soki Tarayyar Turai

Takardar kudi ta Euro Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Matsalar kudade a nahiyar Turai na janyo koma baya a hada-hadar kasuwanci

Ministocin kudi na Najeriya da Afirka ta Kudu sun soki Kungiyar Tarrayar Turai akan kasa magance matsalar bashin dake cigaba da yaduwa a Kasashen dake amfani da kudin Euro.

Pravin Gordhan na Afrika ta Kudu da Ngozi Okonjo Iweala ta Najeriya sun ce rashin daidaiton takardun kudade da kuma farashin kayayyaki suna yin barazana ga cigaban tattalin arzikin Kasashen Afirka.

Mr. Gordhan ya ce matsalar kudade a nahiyar Turai na janyo raguwa akan hada-hadar kasuwanci

Ita kuwa ministar kudi ta Najeriya Mrs. Okonjo Iweala cewa ta yi Kasashe masu tasowa zasu koyi darasi daga Kasashen da suka cigaba a duniya, akan yadda zasu shawo kan matsalar bashi da kuma bunkasa tattalin arzikin su.

Karin bayani