Transparency International ta yanke hulda da FIFA

Shugaban Hukumar FIFA, Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Transparency International ta yanke hulda da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA

Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa a duniya wacce ke baiwa hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA shawara, bayan da batun cin hanci da bada toshiyar baki ya dabaibaye hukumar, ta ce ta yanke hulda da hukumar ta FIFA.

Kungiyar Transparency International ta ce bata ji dadin yadda FIFA taki amincewa da wasu manyan shawarwarin ta biyu ba.

Wannan matakin dai babban koma baya ne ga yunkurin FIFA na kawo sauye-sauye don dawo da martabar ta a duniya.

Babbar jami'a a Kungiyar Transparency International Sylvia Shenk, ta shaidawa BBC cewa hukumar FIFA bata magance matsalolin ta na baya ba

Kawo i yanzu dai Hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA bata maida martani ba .

Karin bayani