Jam'iyyar Islama ce gaba, a zaben Masar

kidaya kuri'u a zaben kasar Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption kidaya kuri'u a zaben kasar Masar

Sakamakon zagayen farko a zaben 'yan majalisa a Misra na nuni da cewa jami'yyu masu ra'ayin Islama ne zasu samu rinjaye a majalisa.

Jamiyyar 'yan uwa musulmi ta kama hanyar lashe yawancin kuri'un da aka jefa.

Jam'iyyar na gabatar da kan ta a matsayin mai matsakaicin ra'ayin kishin Islama, amma duk da haka akwai jam'iyyu masu kaifin kishin Islamar da ke taka rawar gani a zaben.

Jamiyyar ta yi kira ga sauran jamiyyu da su rungumi kaddara.

Sauran jam'iyyun masu sassaucin ra'ayi sun bayana fatan cewar 'yan takararsu zasu tabuka abin kirki a sauran zabukan da za a gudanar a karo biyu.

Karin bayani