Kamfanin Shell ya dakatar da aikace-aikacensa a Syria

Shugaba Asad na Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamfanin Shell ya dakatar da aikace-aikacen sa a Syria

Kamfanin mai na Shell ya dakatar da da ayyukansa a cikin Kasar Syria, saboda sabbin takunkumin da Kungiyar Tarrayar Turai ta kakabawa Kasar, sakamakon amfani da karfi fiye da kima akan masu zangar-zangar adawa da gwamnati.

Wani mai magana da yawun kamfanin shell yace kamfanin ya dauki wannan mataki ne domin yin biyayya ga sabbin takunkumin da Tarayyar Turai ta kakabawa Kasar da kuma kare ma'aikatan sa.

Ana sa ran suma sauran kamfanonin Kasashen Turai da ke aikace-aikace a Kasar Syrian za su bi sahun matakin da Kamfanin Shell ya dauka.

Kasashen Amurka da Turkiyya sun bada sanarwar karin takunkumi akan Kasar Syrian a wannan makon, wadanda suka shafi bangaren bankunan Kasar da kuma daidaikun jama'a.

Ita ma Kungiyar Kassahen larabawa ta kakabawa Syrian nata takunkumin makamancin wannan a makon daya gabata.

Karin bayani