Biden ya bukaci shugaba Assad ya sauka

Hakkin mallakar hoto 1

Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden wanda yayi wata ganawa da mahukunta a kasar Turkiyya, ya ce gwamnatin shugaba Assad a kasar Syria na ruruta wutar tashin hankali mai nasaba da bambancin addini, kuma hakan na yin barazana, ba wai kawai ga zaman lafiya a Syriyar ba, har ma da daukacin yankin.

Ya ce ci gaba da kasancwar su kan karagar mulki na barazanar kara iza wutar rikicin addini, da zata iya watsuwa zuwa sauran kasashen yankin.

Shi dai shugaba Assad na bin akidar Alawite ne, wadda mabiyanta 'yan tsiraru ne a kasar, amma kuma su ke rike da gwamnati.

Galibin 'yan adawar kasar mabiya sunni ne, da kuma suke da rinjaye a kasar.

Su ma kungiyoyin kare hakkin jama'a sun zargi gwamnatin Syriar da daukar matakai da gangan domin cusa zaman fargabar rikicin addini.

Karin bayani