An kai hari da makamai a garin Azare

Wasu jami'an tsaro a Nijeriya
Image caption Wasu jami'an tsaro a Nijeriya

Rahotanni daga jihar Bauchi a Nijeriya na cewa mutane kamar bakwai ne suka rasa rayukansu da suka hada da jami'an tsaro da kuma farar hula, a wani harin bama-bamai na tsakar dare a kan hedikwatar 'yan sanda ta yankin Azare, da kuma wasu bankuna guda biyu.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Bauchi ta bayyana cewa jami'anta sun yi musayar wuta da maharan a lokacin farmakin.

Mazauna garin na Azare sun bayyana cewa sun kwana cikin fargaba a sakamakon harin.

Duk da cewa hukumomi ba su fito sun bayyana wadanda ake zargi da kai harin ba, wasu da suka shaida lamarin sun ce yayi kama da irin wanda ake zargin kungiyar Boko Haram da kai wa a wasu sassan arewacin Nijeriya.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Bauchi Mr Ikechukwu Aduba, ya ce suna ci gaba da bincike.

Karin bayani