Iran ta harbo jirgin leken asirin Amurka

Masana'antar nukiliyar Iran Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masana'antar nukiliyar Iran

Rahotanni daga Iran na cewar dakarun kasar sun harbo wani jirgin saman yakin Amurka mara matuki a cikinsa, a gabashin kasar.

Wasu kafafen yada labarai na kasar ta Iran sun bayyana jirgin da cewa na leken asiri ne, sampurin RQ170.

An kuma ce an gano jirgin ne ba tare an yi masa wani lahani mai yawa ba.

Ya zuwa yanzu ma'aikatar tsaron Amurka a Washington ba ta mayar da martani kan wannan batu ba, sai dai Iran ta yi gargadin cewa, matakan da zata rika dauka, in aka keta ma ta haddi, ba zai tsaya cikin yankin kasarta ba.

A farkon bana Iran ta ce mayakanta sun harbo wasu jiragen yakin Amurka biyu da basu da matuka, wadanda kuma suka shiga yankin kasarta.

Sai dai ba ta gabatar da wata shaidar da zata gasgata ikirarin ba.

Karin bayani