PDP ta lashe zaben gwamnan jihar Kogi

Zabe a Nijeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zabe a Nijeriya

Hukumar zabe a jihar Kogi ta Nijeriya, ta bayyana sunan Kyaftin Idris Wada, dan takarar jam'iyyar PDP mai mulkin jihar, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Sakamakon na nuna cewa ya samu nasara a kananan hukumomi goma sha takwas daga cikin ashirin da daya na jihar.

Takarar dai ta fi zafi ne tsakaninsa da Prince Abubakar Audu na jam'iyyar adawa ta ACN, wanda ya nuna rashin gamsuwa da sakamakon, ya kuma ce zai dauki dukkan matakan da suka dace na kalubalantarsa.

Jihar Kogi na daga cikin jihohi biyar a Nijeriya da aka jinkirta gudanar da zabensu a bara, lokacin da aka yi zaben kasa baki daya, sakamakon wani hukuncin kotu da ya ce gwamnonin jihohin ba su kammala wa'adin mulkin ba.

An dai tsaurara matakan tsaro, tun gabanin zaben, kuma rahotanni daga jihar ta Kogi na cewa komai na tafiya daidai, babu wasu alamun tayar da hankali, bayan bayyana sakamakon zaben.

Karin bayani