Rinjayen jam'iyyar Putin ya ragu a Rasha

Praminista Putin na Rasha Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Praminista Putin na Rasha

Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa jam'iyyar praministan Rasha, Vladimir Putin ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a kasar, duk da cewa ba ta samu rinjaye na yawan kuri'un da aka kada ba.

Dama dai ana ganin zaben, a matsayin zakaran gwajin dafi na farin jin praministan.

Mr Putin zai tsaya takarar shugabancin kasar da za a gudanar nan da watanni ukku masu zuwa.

Kungiya daya tilo mai zaman kanta a kasar ta Rasha dake sa ido kan zabe, ta ce shafinta na intanet , inda take lissafata irin yadda ake yi ma dokokin zabe karan tsaye, a yanzu an masa kutse an durkusar da shi, an kuma toshe shi.

Amurka ta yi korafin cewa ana kuntata ma kungiyar sa idon mai zaman kanta a zaben.

Wakilin BBC a Moscow ya ce an bada rahotannin magudi, yayinda hukumomi ke cewa suna an kwatanta gaskiya da adalci a zaben.

Karin bayani