Jam'iyyar Putin ta fuskanci koma baya a Rasha

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Pira Ministan Rasha, Vladimir Putin

Pira Ministan Rasha, Vladimir Putin ya fuskanci koma baya a zaben 'yan Majalisu da aka gudanar a kasar.

Jam'iyyarsa ta United Rasha ta lashe kashi hamsin ne na kuri'un da aka kada a zaben, wanda kuma ya yi kasa sosai, idan aka kwatanta da zaben da aka gudanar a baya.

Sakamakon zaben dai wani sabon babi ne ga Vladimir Putin.

Ya dai saba da sannin cewa shine dan siyasar Rasha da yafi karfi kuma mafi tasiri a 'yan shekarun da su ka gabata inda kuma yake tafiyar da al'umuran yau da kullum a fagen siyasa.

A yanzu haka dai, jam'iyyarsa ta fuskanci dan tangarda a zaben 'yan majalisu, saboda ba za ta samu yawan kujerun da take da su a da ba.

Kujerun da jam'iyyar ta ke da su a da sun ragu daga kashi sittin da hudu zuwa kashi hamsin cikin dari. Hakan ma ya auku ne duk da zargin da ake yiwa jam'iyyar cewa ta tafka magudi.

Wannan dai babban abun kunya ne ga Mista Putin, ganin cewa nan da watanni uku zai sake tsaya takarar shugban kasa. Yana dai da tabbacin shi zai lashe zaben na shugaban kasa da za'a gudanar a watan Maris din badi. Amma zaben na 'yan majalisu ya fara nuni a cewa al'ummar kasar sun fara gajiya da salon mulkinsa na sama da shekaru goma.

Karin bayani