Ana taro akan makomar Afghanistan

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai, ya ce tallafin kasashen waje, bayan janyewar dakarun da NATO ke jagoranta a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, zai kasance da mahimmanci matuka ga samun zaman lafiya a kasar a nan gaba.

Da yake magana a wajen taron kasashe a birnin Bonn na Jamus, mista Karzai ya yabawa cigaban da aka samu a Afghanistan.

To amma kuma ya jaddada cewa, har yanzu ba a shawo kan matsalar babakeren da 'yan gwagwarmaya suka yi a wasu yankunan kasar ba.

Kasar Pakistan ta kauracewa taron na yau, domin kokawa da kisan sojojinta ashirin da hudu da kungiyar tsaron NATO ta yi a watan da ya wuce.

Karin bayani