Malaman jami'a sun fara yajin aiki a Najeriya

Hakkin mallakar hoto 1

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya, ASUU, ta shiga yajin aiki na sai abinda hali ya yi.

Kungiyar dai na zargin gwamnatin kasar ne da kasa aiwatar da yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma, shekaru biyu da suka wuce.

Yajin aikin dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daliban jami'o'in ke shirin fara jarrabawa.

An jima ana fuskanatar matsalar yajin aikin malamai a jami'o'i a Najeriya.

Shekaru biyun da suka wuce ne gwamnati ta cimma wata yarjejeniyar da a karkashin ta, malaman jami'o'in suka dakatarda wani yajin aiki.

A karkashin waccan yarjejeniyar, gwamnati zata karawa kudaden gudanar da jami'o'in kasar.

Sai dai a cewar malaman, har yanzu gwamnati bata mutunta yarjejeniyar ba.