Kamfanin BP ya zargi Halliburton

Hakkin mallakar hoto BP
Image caption Fashewar batutun mai a tekun Mexico shi ya haddasa tsiyayar mai a tarihi Amurka

Katafaren kamfanin mai na BP ya zargi kamfanin hakar mai na Halliburton da lalata shaidar dake nuna cewa yana da hannu wurin haddasa fashewar bututun mai a tekun Mexico.

Fashewar bututun man da aka yi a tekun Mexico a bara ya haddasa mutuwar mutane goma sha daya.

BP ya bada shaidarsa ce a lokacinda ake sauraren karar da ya shigar a wata kotu dake New Orleans a Amurka.

Kamfanin ya ce da gangan Halliburton ya lalata sakamakon gwajinda aka yi kan simintinsa da aka yi amfani da shi a rijiyar man.

Zarginda kamfanin na BP yayi na zuwa ne yayinda ake sa ran fara sauraren wata karar a watan Febrairu mai zuwa, wadda za ta tantance wanda ke da alhakin haddasa fashewar bututun da ya haddasa tsiyayar mai mafi girma a tarihin Amurka.

Karin bayani