Nasrallah ya yi jawabi a bainar jama'a

Hassan Nasrallah Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hassan Nasrallah

Jagoran kungiyar Hezbollah a Lebanon, Hassan Nasrallah, ya yi jawabinsa na farko a bainar jama'a cikin shekaru da dama.

Ya yi wani dan gajeran jawabi ga dubban magoya bayansa a birnin Beirut domin bikin tinawa da zagayowar ranar Ashura, da 'yan Shi'a ke yi. A jawabin nasa, Hassan Nasrallah, ya ce yana aikewa da sako ne ga wadanda suka yi amannar za su iya yin barazana ga kungiyar Hezbollah.

Hassan Nasrallah ya ce za Hezbollah za taci gaba da jajircewa da rike makamai, kuma yawan 'ya'yan ta sai karuwa yake yayinda suke kara gogewa.

Za'a a iya kirga bayyanar Mr Nasrallah a bainar jama'a tun bayan yakin da kungiyarsa ta gwabza da Isra'ila shekaru biyar din da suka wuce.

Karin bayani