Shirin kyautata lafiyar mazauna yankin Agadez

Masana'antar hako uranium a Arlit
Image caption Masana'antar hako uranium a Arlit

Kamfanin Faransa na AREVA, mai aikin hakar ma'adinai a Arewacin Jumhuriyar Nijar, ya bullo da wani shiri na kula da lafiyar mazauna yankin Agadez.

Kamfanin zai ajiye kwararrun likitoci da kayan aikin da suka dace, domin kula da lafiyar ma'aikatan da ke aikin hako Uranium, da tsofin ma'aikatan kamfanin, da ma mutanen da ke zaune a kewayen wuraren da ake hako uranium din.

Mutanen Agadez dai sun dade suna kokawa da gurbacewar muhallinsu, sakamakon aikace- aikacen kamfanin na AREVA, wadanda suka ce suna janyo masu cututuka iri iri.

A baya dai kamfanin na AREVA ya sha musanta cewa aikace-aikacensa a yankin Arlit, na janyo gurbacewar muhalli, yana mai cewa yana daukan matakan da suka dace na kare lafiyar jamaa da muhallinsu.

Karin bayani