An kama masu zanga zangar zabe a Rasha

Masu zanga zanga a Rasha Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga a Rasha

'Yan sanda a Mosko, babban birnin kasar Rasha, sun kama magoya bayan 'yan adawa kimanin dari biyu da hamsin, ciki har da jagoran 'yan adawa Boris Nemtsov, a kwana na biyu da aka kwashe ana zanga zanga, kan zargin an tafka magudi a zaben majalisar dokokin kasar.

Masu zanga zangar na zargin jam'iyyar praministan kasar, Vladimir Putin ne da tabka magudin.

An dai kawo daruruwan matasa, magoya bayan Putin cikin Masko daga duk fadin kasar domin su ma su nuna goyan bayansu ga Putin.

Praminista Putin dai zai tsaya takarar shugaban kasar, a zaben da za a gudanar cikin shekara mai kamawa.

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha tana bayyana sukar lamirin zaben da Amurka ta yi da cewa, abu ne da ba za a amince da shi ba.

Ranar Lahadi ne aka gudanar da zaben majalisar dokoki, inda rinjayen da jam'iyyar dake mulki ta ke da shi a majalisa ya ragu matuka.

Karin bayani