Standard and Poors na barazana ga kasashen Turai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumar Standard and Poors ta rage darajar wasu kasashen Turai

Hukumar auna karfin kasashe wurin biyan basussuka ta Amurka, wato Standard and Poor's, ta sanyawa kusan daukacin kasashen turai ido na yiwuwar rage masu daraja.

Wannan mataki na nufin, cewa nan da watanni masu zuwa, ta yiwu darajarsu ta karba da biyan bashi ta ragu.

Daga cikin kasashenda wannan abu zai shafa har da kasashen Jamus da Faransa, wadanda suka fi karfin tattalin arziki a nahiyar turai.

Sanarwar da Hukumar ta Standard and Poors, ta zo ne a mawuyacin halin ga Shugabanin kasashen Turai da ke amfani da kudin Euro.

Yana kuma nufin akwai yiwuwar hukumar ta rage karfin kasashe 15 na tarrayar Turai da ta bayyana nan da watanni uku.

Tallafin kasashen Turai

Idan kuma aka rage karfin kasashe kamar su Jamus da Faransa matakin zai yi matukar illa ga tattalin arzikin yankin.

Har wa yau, ganin cewa wannan matakin ba zai shafi kasashen wajen karbar bashi ba.

Zai dai iya shafar yadda kasashen ke bada tallafi ga sauran kasashen Tarrayar Turai da ke fuskantar durkushewa, musamman idan sun kasa sauke nauyin basusukan da ke wuyan su.

Shugaba Sarkozy na kasar Faransa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun fidda wata sanarwa ta maida martani ga Standard and Poor's.

Sun ce sun fahimci barazanar, to amma sun ce sabbin matakan da suka dauka kan kasafin kudin kasashe tarayyar turan, zai karfafa dangantaka a tsakanin kasashe 17 na turai dake amfani da kudin bai daya na euro.

Karin bayani