An yi kokarin satar fita da Saadi zuwa Mexico

Saadi Gaddafi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saadi Gaddafi

Gwamnatin kasar Mexico ta ce ta bankado wani shiri da aka yi na kokarin satar fitar da dan Kanar Gaddafi, watau Saadi Gaddafi domin kai shi kasar Mexico a boye a watan Satumban da ya wuce.

Gwamnatin Mexico ta ce jami'an leken asiri ne suka gano shirin da aka yi, inda kuma za'a hada da wasu iyalan marigaryi Gaddafi, domin kai su kasar ta Mexico da takardun bogi.

Ministan cikin gida na kasar Mexico, Alejandro Poire, ya ce jami'an leken asirin Mexico ne suka gano shirin.

Ana zargin mutanan da suka shirya kaisu, da sayan gidaje a Mexico da dama, ciki harda wani da ke wajen shakatawar nan dake gabar Pacific, inda aka ce fitattun kamar mawakiyarnan Lady Gaga na da gidaje.

A yanzu haka dai Saadi Gaddafi, wanda tsohon kwararran dan kwallo ne ya na zaman daurin talala a Jamhuriyar Nijar.

Karin bayani