Ana neman tallafin abinci a yankin Sahel

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu mata a Somalia, su na jiran tallafin abinci

Wata babbar jami'ar bayar da agaji ta Kungiyar Tarrayar Turai ta ce ana bukatar karin tallafi a kasar Nijar da ma wadansu kasashen yankin Sahel a yammacin Afrika, saboda suna fuskantar matsalar karancin abinci.

Da take jawabi a birnin Landan, Kwamishiniyar Bayar da Agaji Kristalina Georgieva ta ce akwai hasashen da aka yi wanda ya yi nuni da cewa yankin zai yi fama da matsananciyar yunwa a badi muddin ba a magance matsalar ba a kan lokaci.

Kasar Nijar dai ta fuskanci matsalar karancin abinci a shekarar 2005 a yayinda kuma ta fuskanci barazanar sake aukuwar hakan a shekarar 2010.

A bana dai, ganin cewa an samu karancin ruwan sama da kuma matsalar kwari a gonaki, kasar ta kara fitar da sanarwa cewa tana iya fuskantar matsalar karanci abinci, a yayinda kasar Mauritania ma ta yi hakan.

Kwamishiniyar ta nuna damuwa sosai a kan kasashe kamar su Mali da Burkina Faso da kuma arewacin Najeriya, inda ta ce akwai yiwuwar su ma su fuskanci matsalar karancin abinci.

Ta ce a maimakon abin da ya faru a shekara ta 2010, akwai dan tanadi da aka yi na abinci a wadannan yankunan.

Ta ce Tarrayar Turai na sanya ido sosai a kan yara da kuma mata masu juna-biyu, ta yadda za ta tallafa masu kada matsalar ta shafe su sosai.

Wannan kiran da hukumar ta yi na neman taimakon gaggawa ga kasashen yankin Sahel ya zo ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke fama da matsalar karancin abinci a kasar Somalia da kuma matsalar 'yan gudun hijira.

Ana ganin dai wannan matsala wadda ta ki ci ta ki cinyewa na iya shiga shekara mai zuwa.

Karin bayani