Shugaba Assad ya musanta murkushe masu zanga zanga

Shugaba Bashar al-Assad Hakkin mallakar hoto AFP SANA
Image caption Shugaba Bashar al-Assad

Shugaban Syria, Bashar al-Assad, ya musanta cewa shi ne ya ba sojojin kasar umurnin su kashe, ko kuma su kuntatawa masu zanga zangar nuna kyamar gwamnati.

A hirarsa ta farko da kafofin yada labaran Amirka, tun bayan barkewar rikici a Syria a watan Maris, shugaba Assad ya gayawa kafar yada labaran ABC cewa, lallai ana tashe tashen hankula a yawancin kasar, to amma a zahiri al'amurra na daidaita.

Bashar al-Assad ya ce, ba shi ke da alhakin tashe tashen hankulan ba, kuma yayi iya kokarinsa wajen kare jama'arsa.

Amma kuma yayi nadama game da hasarar rayukan da aka yi.

Majalisar dinkin duniya ta kiyasta cewa, fiye da mutane dubu hudu ne aka kashe a Syriar, a watanni goman da aka kwashe ana ta zanga zanga.

Karin bayani