Mutane biyu sun hallaka a zanga zanga a Zinder

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Image caption Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

Rahotanni daga birnin Damagaram na jamhuriyar Nijar sun ce, wata mata ta rasa ranta a yau, bayan harbin da jami'an tsaro suka yi, a lokacin da wasu dalibai da jama'ar gari ke gudanar da wata zanga-zanga.

An kona ofishin 'yan sanda na babbar kasuwar Dole, kuma an rika kona tayoyi a kan hanyoyi.

A jiya ma wani dalibi ya rasa ransa, sakamakon harba barkonon tsohuwa da jami'an tsaron suka yi.

Rahotanni sun ce daliban sun yi zanga-zangar ce, domin nuna bacin ransu da yadda hukumomi ke cigaba da tsare wasu abokan su da aka kama a kwanan baya, wadanda kuma suka gurfana jiya a kotu.

Yanzu dai kura ta lafa, kuma an karfafa matakan tsaro a birnin. A cikin wata hira da BBC, wani jami'i a fadar gwamnan jahar ya nuna cewa, zanga zangar daliban na da nasaba da siyasa, ba wai don kishin 'yan uwansu dalibai ba.

Rahotanni daga Yamai na cewa wasu dalibai sun kona tayoyi a wurare daban daban, domin nuna goyon baya ga dalibai 'yan uwansu na birnin na Damagaram. Wasu kungiyoyin farar hula sun soma nuna fargabarsu, kuma suka yi kira ga gwamnati da ta dauki matakan maido da kwanciyar hankali a Damagaram din.

Karin bayani