Ana kokarin sassanta rikici a Damagaram

Mahamadou Issoufou
Image caption Mahamadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar a yau ne praministan kasar, Briji Rafini ya kai ziyara birnin Damagaram, wanda ya yi fama da tashin hankali a sakamakon zanga -zangar kwanaki uku a jere.

A lokacin ziyarar Praminista Rafini ya gana da mahukuntan jihar, da sauran masu fada-aji, a kokarin lalubo hanyar kawo karshen wannan zanga zanga, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane biyu, tare da kona wani banki da wani ofishin 'yan sanda.

Praministan ya ce shugaba Mahamadou Issoufou ne ya tura su Damagaram din don mika sakon ta'azziya ga iyalan wadanda suka rasa rayikansu a lokacin zanga-zangar, yana mai cewa gwamnati za ta gudanar da bincike a kan al'ammarin da zummar hukunta wadanda ke da hannu a ciki.

Ya zuwa lokacin sallar azahar yau Alhamis dai an samu rahotannin lafawar al'amura, yayinda sojoji ke ta kai-kawo a birnin.

Wakiliyar BBC ta ce wadansu kungiyoyin farar hula ne suka nemi a ba su izinin su fita don nuna rashin jin dadinsu da abin da ya faru jiya da shekaran jiya amma aka hana su; daga nan ne wadansu mutanen suka yi amfani da wannan dama suka yi ta jefe-jefe da kone-konen tayoyi.

Akasarin wadanda wakiliyar BBC ta tattauna da su sun ce dalilin fitowarsu shi ne nuna rashin jin dadinsu da kisan mutane biyun da aka yi, su kuma bukaci gwamnan jihar ya yi murabus.

Sai dai gwamnan jihar ta Damagaram, Alhaji Umarou Seydou Issaka, ya ce hukumomi ba su san abin da ya haddasa zanga-zangar ba.

A cewarsa, "idan za a yi wani abu irin wannan kamata ya yi a rubuta takarda a kai wajen magajin gari; in taro ne na lumana su fada.

"Amma wadanda suka ce 'yan makaranta ne su za su [gudanar da zanga-zanga] sun ga ba su yi bisa ka'ida ba, ko kuma an hana, sai suka janye nasu.

"Amma wadanda suka gudanar da zanga-zangar ba su ajiye takarda ba, na tambayi magajin gari ya ce shi ma bai san yadda aka yi ba".

Karin bayani