An datse mahadar arewa da kudancin Najeriya

Tsofaffin 'yan gwagwarmayar Naija Delta Hakkin mallakar hoto b
Image caption Tsofaffin 'yan gwagwarmayar Naija Delta suna mika makamansu

Rundunar 'yan sanda ta Najeriya ta tare wani ayarin matasa da ke ikirarin cewa tsofaffin masu gwagwarmayar 'yanta yankin Naija Delta ne wadanda suka ajiye makamai a gadar Koton-Karfe a kan hanyarsu ta zuwa Abuja.

Rahotanni daga Jihar Kogi na nuna cewa tsofaffin masu gwagwarmayar su kimanin dari biyu sun niko-gari ne da nufin yin wata zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu game da gazawar gwamnatin tarayya wajen cika musu alkuwuran da ta yi a shirinta na yi musu afuwa

'Yan sandan sun tare ayarin ne ta hanyar datse gadar ta Koton-Karfe wadda ke kusa da garin Lokoja, inda suka nemi tsofaffin masu tayar da kayar bayan su juya amma suka ki, daga nan kuma hanyar ta cushe.

Daya daga cikin masu ababen hawan da lamarin ya rutsa da su, Mallam Abbas Maikarfi, ya samu damar yin tozali da wadansu daga cikin tsofaffin masu gwagwarmayar:

"Ba su rike makamai ba, suna dauke ne da {kwalaye} masu rubutun cewa sai an cika musu alkawuran da aka yi musu", in ji Mallam Abbas.

Ya kuma kara da cewa "ba su taba fasinjoji ba, sun dai tsare hanya sun ce ba shiga ba fita".

Kwamishinan 'yan sandan Jihar Kogi, A.J. Abakasanga ya shaidawa BBC cewa jami'ansa sun tare matasan ne saboda ba su gamsu da dalilan da suka gabatar musu na zuwa Abuja ba.

Ya kara da cewa masu gwagwarmayar sun ce za su Abuja ne domin su samu abin yin bikin Kirsimati da iyalansu, kuma wannan ba dalili ba ne.

Sai dai ya tabbatar da cewa matasan ba su nuna alamar tayar da rikici ba, don haka ne 'yan sanda ke lallaminsu domin su hakura su juya, amma idan abin ya gagara to za su kai ga yin amfani da karfi domin su bude hanyar.

Rahotanni dai sun ce ya zuwa yanzu hanyar ta dan bude, ababen hawa kuma sun fara wucewa.

Mai bai wa Shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara a kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak, ya ce gwamnatin tarayya na nan tana ci gaba da gudanar da shirin afuwar ta hanyar koya wa matasan san'o'i kuma idan kowa ya yi hakuri zai ci gajiyar shirin.

A baya dai gwamnatin Najeriyar ta fito ta ce ba ta da sauran tsofaffin masu gwagwarmayar da ba ta shigar da su cikin shirin nata na yi musu afuwa ba, saboda wa'adin da ta ba su na shiga shirin ya cika, kuma duk wanda ya yi jinkirin shiga shi ya jiwo.

Wanna dai ba shi karo na farko ba da matasan ke zuwa Abuja don yin irin wannan zanga-zangar.