Ana tafka kazamin fada a birnin Mogadishu

Mayakan Al-Shabaab Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana kafsa kazamin fada da Kungiyar Al-Shabaab

Ana yin wani kazamin fada a Mogadishu babban birnin Somalia, yayinda dakarun dake goyon bayan gwamnatin rikon kwarya suka kafsa da mayakan Kungiyar 'yan gwagwarmayar Islama ta Al-Shabaab.

An dai yi amfani da manyan makamai , kuma an ce fadan a yankin arewacin Mogadishu, shi ne mafi kamari a cikin watanni.

Dakaru daga dakarun kiyaye zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afrika a Somalia sun shiga cikin farmakin , wanda ya biyo bayan hare-haren sari- ka- noke da Kungiyar ta Al-Shabaab ke kaiwa -- hade da wani samame a wani sansani a gundumar Wadajir da sojojin Kungiyar Tarayyar Afrikan ke iko da ita.

Karin bayani