Rod Blagojevich zai shafe shekaru 14 a gidan yari

Tsohon Gwamnan Jihar Illinois Rod Blagojevich Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kotu ta yankewa Rod Blagojevich hukuncin shekaru 14 a gidan yari

Wata kotu a Amurka ta yanke wa tsohon Gwamnan Jihar Illinois, Rod Blagojevich hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari saboda cin hanci

An same shi da laifin kokarin sayar da tsohuwar kujerar Shugaba Obama ta majalisar dattawa.

An dai kama shi ne shekaru ukun da suka wuce, kuma da farko ya musanta aikata duk wani abun da bai dace ba.

To amma a lokacin da aka yanke masa hukuncin , ya ce ba wanda zai zarga illa kansa.

Sai dai Alkalin kotun ya ce ya makara wajen neman gafara.

Andy Shaw shi ne Shugaban Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta Illinois, kuma ya ce shara'ar Mr Blagojevic za ta sa 'yan siyasa su shiga taitayinsu.

Karin bayani