Zaben Congo ya haifar da zanga-zanga a Burtaniya

Shugaba Joseph Kabila na Congo Hakkin mallakar hoto
Image caption Yau ake sa ran bayyana sakamakon zaben Kasar Congo

'Yansanda a Burtaniya sun ce masu fafutuka daga Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo sun hana wani jirgin kasa motsawa a wata tashar jiragen kasa dake birnin Landan.

Ana jin masu fafutukar dai sun latsa kararrawar neman agajin gaggawa ne domin nuna rashin jin dadinsu game da yadda aka gudanar da zaben Shugaban Kasa a Kasarsu.

'Yansanda sun yi awon gaba da masu fafutukar a wani jirgin da babu kowa cikinsa, sai dai ba a kama kowa ba.

Jami'an zaben kasar Congon dai sun sake jinkirta bayyana sakamakon zaben.

Shugaban Hukumar zaben Kasar, Daniel Ngoy Mulunda ya bayyana dalilin da ya sa aka sake jinkirta bayar da sakamakon.

Ya ce, 'dole ne mu tantance sakamakon da muka samu ta baka da wanda muke da shi a kan takardu, a don haka dole mu tabbatar cewar sakamakon da muka bayyana na gaskiya ne, wanda kuma keda nagarta'.

Galibin kuri'un da aka kidaya dai sun nuna cewa Shugaba Joseph Kabila nada babbar rata a kan babban abokin hamayyarsa, Etienne Tshisekedi.

To amma magoya bayan Mr. Tshisekedi sun yi barazanar kwarara kan tituna, idan aka ayyana cewar Mr. Kabila ne ya lashe zaben.

Karin bayani