Amincewa da sabuwar yarjejeniyar Tarayyar Turai ya ci tura

Nicolas Sarkozy da Angela Merkel Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amincewa da wata sabuwar yarjejeniyar Turai na fuskantar cikas

Bayan tattaunawar talatainin dare a birnin Brussels, Shugaba Sarkozy na Faransa ya ce kokarin samun dukkanin Kasashe 27 na Kungiyar Tarayyar Turai su amince da wata sabuwar yarjejeniyar Turai ya ci tura.

Mr. Sarkozy ya ce maimakon haka, Kasashe 17 dake amfani da kudin Euro za su sa hannu a kan wata yarjejeniyar da za ta hada gwamnatocinsu dake da aniyyar daidaita kudin, yayinda ake fuskantar matsalar bashi.

Yarjejeniyar za ta hada da duk wata Kasa wakiliyar Kungiyar EU dake son shiga. Shugaban na Faransa ya ce bukatar Burtaniya na wareta daga cikin sharuddan kudi ya sa samun cikakkiyar yarjejeniyar ya yi wuya.

Wakilin BBC ya ce, 'a kodayaushe dai Firayim Ministan Birtaniya David Cameron yana dari-dari wajen amincewa da wani sauyin tsarin mulki wanda yake jin zai baiwa Brussels iko, don haka ba zai goyi bayan shirin ba''