Yan fashi sun kashe mutane a Sokoto

'Yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sandan Najeriya

Rahotanni daga jahar Sakkwato sun ce akalla mutane biyu ne suka mutu wasu kuma biyu suka samu raunukka a wani harin da wasu 'yan fashi da makami suka kai kan wani kauye dake gabashin jahar da tsakar daren jiya.

Wadanda suka shaidi lamarin sunce hakama maharan sun yi awon gaba da dukiyar da ba' a san yawan ta ba daga kauyen na Gatawa mai nisan fiye da kilomita 130 daga babban birnin jahar.

Hare-hare akan kauyuka da kuma garuruwa dake wajen manyan birane na karuwa a arewacin Najeriya inda 'yan fashi da makami ke anfani da damar rashin isassun matakan tsaro acan suna kai farmaki kan mazauna kauyukkan.

A waje daya kuma wasu da ake zargin 'yan fashin cikin teku ne sun harbe har lahira wasu 'yan sanda biyu a garin Nembe dake jahar Bayelsa a kudu maso kudancin Najeriya.

Karin bayani